Shahararriyar mawakiyar Afrobeats ta Najeriya, Tiwa Savage, ta bayyana yadda take kewar kulawa da goyon bayan da take samu daga Don Jazzy da sauran ‘yan uwanta na tsohuwar kamfanin waka ta Mavin Records.
Da take magana a shirin Afrobeats Intelligence Podcast, Tiwa Savage ta ce sai bayan ta bar Mavin ne ta fahimci muhimmancin samun kamfanin waka mai kula da jin dadin mawaki.
Ta bayyana cewa idan wata matsala ko cece-kuce ta taso a kafafen sada zumunta, tana zuwa dakin Don Jazzy domin neman shawara da kwanciyar hankali tare da sauran mawakan Mavin.
“Wanda ka ke karkashinsa a harkar waka yana da matukar muhimmanci, kuma ban gane hakan sosai ba sai bayan na bar Mavin. Duk lokacin da wata matsala ta taso a intanet, zan je dakin Don Jazzy, mu zauna tare da sauran mawakan Mavin muna tattaunawa,” in ji ta.
Tiwa ta kara da cewa tana samun damar bayyana damuwarta a fili har ma ta yi kuka idan ya cancanta, amma yanzu hakan ya canja bayan komawarta wata kamfanin waka ta kasashen waje.
“Idan ina bukatar yin kuka, zan yi kuma mu magance matsalar tare. Amma yanzu ina karkashin kamfanin kasashen waje, ba su damu da rayuwarka ta kashin kai sosai ba. Ba zan iya zuwa ofishin Empire na yi kuka ba. Ina kewar wannan bangaren,” ta fada.
Tiwa Savage ta shiga Mavin Records a shekarar 2012 kafin daga bisani ta bar kamfanin a 2019 domin kulla yarjejeniya da Universal Music Group.
