Premiere Academy tare da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ta hannun United Nations Information Centre (UNIC) Abuja, sun gudanar da zagaye na biyu na taron Premiere Academy International Model United Nations (PAIMUN) General Assembly a hedikwatar MDD da ke Abuja, inda aka yaba wa makarantar kan wannan tsarin ilmantarwa.
Shirin PAIMUN, wanda aka ƙaddamar a 2025 domin murnar cikar Majalisar Dinkin Duniya shekaru 80, yana nufin koya wa dalibai yadda tsarin Majalisar Dinkin Duniya ke aiki ta hanyar kwaikwayo, domin fahimtar diflomasiyya, tattaunawa da yanke shawara a matakin duniya.
Taron na bana da aka gudanar a ranar Alhamis 14 ga Mayu, 2026, ya gudana ne da taken: “Sauyin fasahar dijital a fannin ilimi a matsayin hanyar bunkasa ci gaba mai ɗorewa.”
Dalibai 109 daga makarantar Abuja sun halarci taron, inda suka wakilci kasashe mabanbanta a matsayin jakadun Majalisar Dinkin Duniya a zaman kwaikwayo na babban zauren MDD.
An fara taron ne da sakon bidiyo daga Sakatare-Janar na MDD, António Guterres, wanda ya jaddada muhimmancin fasahar zamani wajen inganta ilimi da ci gaba mai ɗorewa.
Wakiliyar MDD a Najeriya, Ms Elsie Attafuah, ta bayyana shirin a matsayin wata muhimmiyar hanya ta horar da matasa kan shugabanci, diflomasiyya da zaman lafiya. Ta kuma bayyana cewa gibin fasahar zamani da karancin ilimin dijital na daga cikin manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
A nasa jawabin, Shugaban Makarantar Premiere Academy, Chris Akinsowon, ya gode wa MDD bisa haɗin gwiwa, yana mai cewa fasahar zamani ta sauya tsarin ilimi, musamman bayan barkewar COVID-19, inda aka fahimci muhimmancin koyarwa ta dijital.
Ya kara da cewa irin wannan haɗin gwiwa yana taimakawa wajen gina shugabannin gaba da inganta ilimi fiye da tsarin aji na gargajiya.
