Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya, Trabzonspor, ta sanya farashin euro miliyan 40 kan matashin ɗan wasan baya na Najeriya, Chibuike Nwaiwu, bayan nuna bajinta a kakar wasa ta bana.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗan wasan mai shekara 22 ya koma Trabzonspor ne daga Enyimba a watan Janairu kan kuɗin euro miliyan 5.5, amma cikin kankanin lokaci ya zama ɗan wasa na farko a kungiyar.
An ce wasu kungiyoyi sun riga sun yi tayin kusan euro miliyan 20, amma Trabzonspor ta ƙi amincewa, tana mai dagewa kan farashinta na euro miliyan 40.
Idan aka sayar da shi kan wannan farashi, zai zama cinikin da ya zarce na baya-bayan nan a tarihin ƙungiyar, wanda ya shafi mai tsaron gida Uğurcan Çakır da ya koma Galatasaray kan euro miliyan 27.5.
Nwaiwu ya samu yabo saboda iya taka leda a matsayin mai tsaron baya na tsakiya da kuma dan wasan tsakiyar fili na kariya, tare da ƙwarewa a jiki da kwantar da hankali a wasa.
Kungiyoyi irin su Bayer Leverkusen da Fulham an ce suna sa ido kan halin da yake ciki.
Duk da haka, Trabzonspor na da kwangila mai tsawo da shi, wanda zai sa su iya riƙe shi ba tare da matsin lamba ba, yayin da shi kansa ɗan wasan bai nuna sha’awar barin kungiyar nan da kusa ba.
