Wasu ‘yan takarar kujerar majalisar wakilai ta jam’iyyar APC a mazabar Otukpo/Ohinmini da ke jihar Benue sun kalubalanci sakamakon zaben fidda gwani da Blessing Onuh, ‘yar tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ta lashe.
Lawrence Onoja Jnr, dan marigayi Manjo Janar Lawrence Onoja, tare da wani dan takara, Andrew Abu, sun kai korafi zuwa sakatariyar APC da ke Makurdi, inda suka bukaci a binciki yadda aka gudanar da zaben.
Sun zargi magoya bayan Blessing Onuh da kwace kayan zabe tare da yin magudi wajen tattara kuri’u, suna cewa adadin kuri’un da aka bayyana ta samu ya fi yawan rajistattun mambobin jam’iyyar da ke yankin Otukpo da Ohinmini baki daya.
Lawrence Onoja ya bayyana cewa an karya tsarin rabon mukamai na yankin, sannan ya ce maimakon gudanar da zaben a rumfunan mazabu kamar yadda doka ta tanada, an mayar da wurin zaben zuwa wani otel.
Shi ma Andrew Abu ya goyi bayan wannan zargi, yana mai cewa dole ne jam’iyyar ta mutunta tsarin rabon mukamai domin tabbatar da adalci.
Duk da haka, su biyun sun bayyana kwarin gwiwar cewa kwamitin sauraron korafe-korafen jam’iyyar zai yi adalci tare da duba koken nasu yadda ya kamata.
Lamarin ya kuma sake tayar da tsohuwar takaddama ta siyasa tsakanin iyalan David Mark da Lawrence Onoja, wadanda suka taba fafatawa sau da dama kan kujerar Sanatan Benue ta Kudu a baya.
