Ana ci gaba da samun ɗumbin farin ciki gabanin gudanar da gasar ninkaya ta makarantu ta Ikoyi Club/Zenith Bank karo na tara, wadda za a gudanar ranar 23 ga Mayu, 2026, a sashen ninkaya na Ikoyi Club 1938.
Gasar, wadda ta zama ɗaya daga cikin manyan gasannin ninkaya na yara a Najeriya, na ba matasa damar nuna ƙwarewarsu tare da bunƙasa sana’arsu a harkar wasanni.
Fiye da makarantu 20 ne ake sa ran za su halarci gasar ta bana, inda masu shirya taron suka bayyana cewa za a sha gasa mai zafi a fannoni daban-daban.
‘Yan wasa za su fafata a wasannin freestyle, breaststroke, backstroke, butterfly, da individual medley, tare da tsara tazarar gasar gwargwadon shekaru.
Zenith Bank na ci gaba da tallafawa gasar, abin da masu shirya taron suka ce ya taimaka wajen bunƙasa ta tsawon shekaru.
Shugaban sashen ninkaya na Ikoyi Club 1938, Akinbulejo Onabolu, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda gasar ke samun karɓuwa sosai.
Ya ce gasar na daga cikin manyan shirye-shiryen kulob ɗin wajen gano da haɓaka sabbin hazikan ‘yan ninkaya.
Onabolu ya kuma yaba wa Zenith Bank bisa goyon bayan da take bayarwa wajen cigaban wasannin yara.
Masu shirya taron sun ce gasar za ta ƙarfafa gasa mai anfani tsakanin makarantu tare da taimakawa wajen bunƙasa harkar ninkaya a Najeriya.
Ana sa ran iyaye, masu sha’awar wasanni, da masu ruwa da tsaki a harkar ninkaya za su halarta daga sassa daban-daban na Lagos da ma ƙasar baki ɗaya.
