Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya bayyana cewa ya samu ribar N355.5 biliyan bayan haraji a zangon farko na shekarar 2026, wanda ke nuna ƙaruwa da kusan kashi 165.9% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Duk da wannan gagarumar ribar, kamfanin ya yi gargadin cewa hauhawar farashin man diesel na iya rage ribar sa a watanni masu zuwa.
A rahoton da ya fitar a ranar Laraba, MTN ta ce tana sa ran ribar aiki (EBITDA margin) za ta ragu da kusan kashi 1.8 zuwa 2.0 idan farashin diesel ya kai kusan N2,000 a kowace lita a rabin ƙarshen shekarar.
Kamfanin, wanda ke da kusan masu amfani miliyan 89.5, yana da sama da mastoci 20,000 a fadin Najeriya, yawancinsu na dogaro da janareta saboda ƙarancin wutar lantarki mai dorewa.
Shugaban kamfanin, Karl Toriola, ya ce suna ci gaba da sa ido kan sauye-sauyen tattalin arziki da suka haɗa da farashin makamashi da dokoki.
Tsadar Diesel na Ƙara Matsin Lamba
Rahoton ya nuna cewa rikicin makamashi da sauyin farashin mai a duniya na daga cikin abubuwan da ke ƙara tsadar aiki ga kamfanonin sadarwa a Najeriya.
An bayyana cewa matsalolin da suka faru a kasuwar mai ta duniya, musamman rikice-rikicen siyasa tsakanin ƙasashen waje, sun sa farashin danyen mai ya haura dala 100 a kowace ganga, abin da ya jawo tashin farashin man fetur da diesel a Najeriya.
A cikin ƙasar, farashin diesel ya kai tsakanin N1,250 zuwa N1,750 a wasu wurare, yayin da wasu rahotanni ke nuna cewa zai iya ƙara hawa.
Babbar Kalubale Ga Sashen Sadarwa
Rahotanni sun nuna cewa kamfanonin sadarwa a Najeriya na amfani da sama da lita miliyan 40 na diesel duk wata domin kunna mastoci, saboda rashin ingantaccen wutar lantarki daga grid.
Wannan na nufin sama da lita miliyan 480 a shekara, tare da kashe kuɗi da ya zarce dala miliyan 350 a kowace shekara.
Zuba Jari Duk da Matsaloli
Duk da kalubalen, MTN ta ƙara zuba jari sosai inda kashe kuɗin jarinta ya tashi da kusan kashi 92.8% zuwa N390.3bn a Q1 2026.
Kamfanin ya ce yawancin wannan kuɗi ya tafi wajen faɗaɗa hanyar sadarwa, musamman fibre internet da fixed wireless services domin inganta intanet a fadin ƙasar.
