Shugabar Sashen Sadarwa na Kamfanin Bi-Courtney Aviation Services Limited, Ajoke Yinka-Olawuyi, ta kare matakin karin kudin filin ajiye motoci da aka yi a Murtala Muhammed Airport 2 (MMA2), Lagos, inda ta ce ba don neman riba aka yi hakan ba, sai don dawo da filin zuwa yadda aka tsara shi tun farko.
Ta bayyana hakan ne a shirin Arise TV a ranar Alhamis, inda ta ce an yi gyaran farashin ne domin rage cunkoso da kuma tabbatar da cewa filin yana aiki ne a matsayin na “tsayawa na ɗan lokaci” (short-stay parking) ga masu amfani da filin jirgin.
A cewarta, tsawon shekaru an rika amfani da filin ta hanyar da ba ta dace ba, inda wasu direbobi ke barin motoci na dogon lokaci a wurin.
“Ba batun samun kuɗi ba ne. Manufar ita ce a mayar da filin yadda aka tsara shi tun farko, wato na ɗan gajeren lokaci, domin sauƙaƙa shiga tashar jirgin,” in ji ta.
Ta ce kafin a yi sabon tsarin kudin, ana samun motocin kusan 300 da aka ajiye a filin har na tsawon dare, wasu har makonni, wasu kuma har watanni da ma shekara guda.
“Ba gareji ba ne. A wasu lokuta har shekara guda ana barin mota a wurin,” in ji ta.
Ta kuma ce wannan matsalar ta haifar da cunkoso sosai a wajen sauke fasinjoji, wanda ke wahalar da masu amfani da filin jirgin.
Ta bayyana cewa MMA2 na aiki kusan shekara 19, kuma babban burinsu shi ne samar da ingantaccen tsarin hidima ga fasinjoji tare da tsaro da sauƙin amfani.
Sai dai sabon tsarin kudin filin ajiye motoci ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, inda wasu ke cewa ya yi tsada sosai kuma yana matse masu amfani da filin jirgin.
