Jam’iyyar APC mai mulki ta fuskanci zarge-zarge cewa gwamnoninta sun yi ƙoƙarin siyan fom ɗin takara na zaɓen 2027 da yawa domin raba wa ‘yan takarar da suke so, musamman na Majalisar Tarayya.
Wannan ya sa jam’iyyar ta sauya tsarin ta, ta saka bayanan asusun banki domin kowa ya biya kai tsaye.
Rahoton ya nuna cewa hakan ya jawo rikici da rashin jin daɗi a tsakanin ‘yan majalisa, inda wasu ke ganin gwamnoni za su iya rinjayar wanda zai samu tikitin takara a jihohi.
A wani taro da Shugaba Bola Tinubu ya yi da gwamnonin APC, an ce ya ba su damar su jagoranci tsarin fitar da ‘yan takara a jihohinsu, ta hanyar ko dai zaben tursasawa (consensus) ko kai tsaye.
Wannan mataki ya sa wasu ‘yan majalisa suka fara nuna fargaba, saboda suna ganin za a iya barin su a baya duk da goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar.
Jam’iyyar APC ta kuma tabbatar da cewa fom ɗin takara
a bude yake ga kowa, kuma za a yi sahihin zabe na cikin gida (primaries) a ranar 15 zuwa 23 ga Mayu 2026, dangane da matakin zabe.a
Ana ganin cewa lamarin yana haifar da rikici da tattaunawa mai zafi a siyasar APC gabanin zaɓen 2027.