Ƙungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona ta tabbatar da cewa matashin tauraro Lamine Yamal ba zai kara buga sauran wasannin LaLiga na kakar 2025–26 ba, bayan ya samu raunin cinya (hamstring injury).
Matashin ɗan wasan mai shekaru 18 ya samu raunin ne a lokacin da yake zura kwallo ta bugun fanareti a wasan da Barcelona ta doke Celta Vigo da ci 1-0, wasan da ya taimaka wajen ci gaba da fafutukar lashe gasar lig.
A cikin sanarwar likita da Barcelona ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa:
“Binciken da aka yi ya tabbatar cewa ɗan wasan ƙungiyar farko Lamine Yamal yana da raunin hamstring a ƙafarsa ta hagu (biceps femoris muscle).”
Kulob ɗin ya ƙara da cewa za a bi tsarin jinya na “conservative treatment,” ma’ana ba za a yi masa tiyata ba, sai dai zai yi gyaran jiki da hutu har ya warke.
Wannan rauni ya kawo ƙarshen fatan ganin Yamal a sauran wasanni shida na lig, ciki har da babban wasa na El Clásico da Real Madrid a Camp Nou ranar 10 ga Mayu.
Rashin Yamal babban rauni ne ga Barcelona, musamman a lokacin da take fafutukar kare kambun gasar. A karkashin kocin Hansi Flick, kulob ɗin na fuskantar matsin lamba wajen ci gaba da gasar.
Sai dai akwai ɗan haske ga magoya baya, domin rahoton likita ya nuna cewa ana sa ran Yamal zai murmure kafin gasar Kofin Duniya (World Cup).
Likitan kwallon kafa sun bayyana cewa irin wannan jinya yawanci na buƙatar hutawa, gyaran jiki, da kuma dawowa sannu a hankali cikin horo.
Barcelona yanzu za ta dogara da ’yan wasa kamar Robert Lewandowski da Fermín López domin cike gurbin da Yamal ya bari, yayin da take ƙoƙarin ci gaba da matsin lamba kan Real Madrid da ke saman teburin da maki uku.
Yanzu haka, wasan El Clásico na 10 ga Mayu ya zama mai matuƙar muhimmanci—amma Yamal zai kalla ne daga gefe.
