Gwamnatin Amurka ta dauki sabon mataki da zai sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa amfani da cannabis (marijuana) domin dalilai na likitanci, bayan ta sake tsara matsayin dokar da ke kula da shan miyagun ƙwayoyi a ƙasar.
A cewar sanarwar da ofishin United States Department of Justice ya fitar a ranar Alhamis, an sauya matsayin marijuana daga rukunin “Schedule I” zuwa “Schedule III” a karkashin tsarin rarraba miyagun ƙwayoyi na Amurka.
Wannan mataki na nufin cewa an rage matsayinta daga jerin kwayoyi da ake ganin ba su da amfanin likitanci kwata-kwata, zuwa rukuni da ke da “matsakaicin ko ƙarancin haɗarin jaraba”, wanda zai kuma ba da damar ƙarin bincike kan amfani da ita a fannin lafiya.
A baya, United States Drug Enforcement Administration (DEA) ta sanya marijuana a cikin “Schedule I”, wato rukuni na kwayoyi da ake ɗauka a matsayin masu haɗari sosai kuma ba su da amfanin likita, kamar heroin da methamphetamine.
A sabon tsarin, sauyin ya bude ƙofa ga ƙarin binciken kimiyya kan tasirin cannabis, tare da ba likitoci damar yanke shawara bisa ƙarin hujjojin lafiya wajen kula da marasa lafiya.
Mataimakin babban lauyan gwamnati mai riƙon ƙwarya, Todd Blanche, ya ce matakin zai “faɗaɗa damar marasa lafiya samun magunguna tare da ba likitoci damar yanke shawara bisa ingantaccen ilimin likitanci.”
Wannan sauyi ya biyo bayan umarnin shugaban ƙasa Donald Trump da ya bayar a watan Disamba, inda ya bukaci a ƙara bincike kan amfani da marijuana a fannin magani.
Masana harkar lafiya da manufofin jama’a na ci gaba da bibiyar wannan sauyi, wanda ake ganin zai iya shafar yadda ake kula da marasa lafiya da kuma dokokin amfani da cannabis a nan gaba.
