Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti, ya kaddamar da aikin gina gidaje 1,200 a birnin Umuahia, wanda ya kawo karshen shafe shekaru 18 ana dakatar da aikin.
BAYANIN AIKIN
Wannan aikin yana cikin shirin Federal Housing Authority (FHA) Renewed Hope Housing Scheme, wanda ya sanya Abia cikin jihohin farko da suka fara aiwatar da shirin a Najeriya, kuma ita ce jiha ta farko a Kudu Maso Gabas da ta fara shi.
KALAMAN GWAMNA OTTI
A wajen kaddamarwar, Gwamna Otti ya ce:
“Wannan aikin yana da nasaba da jin dadin al’ummarmu. Dukkan abubuwa kamar siyasa, kabila ko addini suna zuwa baya.”
Ya ce gwamnatin jihar ta samu filin ne bayan tattaunawa da hukumar FHA a shekarar 2024, wanda ya kai ga amincewar gwamnatin tarayya.
Biyan Diya
Gwamnatin Abia ta bayyana cewa:
An biya diyya ga fiye da 800 daga cikin kusan 900 da abin ya shafa
Filin aikin yana da girman hekta 100
BAYANIN FHA
Shugaban hukumar FHA, Oyetunde Ojo, ya ce zaɓin Umuahia ya samo asali ne daga yadda gwamnatin Abia ta nuna cikakken shiri da hadin kai.
Ya ce:
“Ba kawai gidaje muke ginawa ba, muna gina sabon tsari na birni mai inganci.”
MA’ANAR AIKIN
Shirin na da nufin: ✔️ Rage matsalar gidaje a Najeriya
✔️ Samar da ayyukan yi
✔️ Taimakawa bunkasar tattalin arziki a yankin
