Sojojin ruwa na Amurka sun ce sun tare tare da dakatar da wani jirgin ruwan kasuwanci mai tutar Iran a Tekun Arabiya, kamar yadda Rundunar Sojojin Amurka ta Tsakiya U.S. Central Command ta bayyana.
A cikin sanarwar da CENTCOM ta fitar, ta ce dakarun Amurka da ke aiki a Tekun Arabiya sun aiwatar da matakan hana zirga-zirgar jirgin ruwan da ke kan hanyar zuwa tashar Bandar Abbas a Iran.
Sanarwar ta bayyana cewa jirgin ruwan mai suna M/V Touska, wanda ke dauke da tutar Iran, ya kasance yana tafiya a cikin Tekun Arabiya da gudun knots 17.
Rahoton ya ce jirgin ruwan ya ki bin umarnin da aka ba shi sau da dama na tsawon kusan awanni shida, duk da gargadin da sojojin Amurka suka yi masa.
Bayan haka, rundunar ta umurci ma’aikatan jirgin da su fice daga dakin injin jirgin, sannan ta yi harbi da makami mai nau’in 5-inch MK 45 a cikin sashin injin domin dakatar da motsinsa.
Daga bisani, sojojin ruwa na Amurka da dakarun Marines na 31st Marine Expeditionary Unit sun hau jirgin domin tabbatar da iko a kansa, inda jirgin yanzu yake hannun Amurka.
CENTCOM ta ce wannan mataki an dauke shi cikin tsari, kwarewa da kuma daidaito domin tabbatar da bin umarni da doka a yankin.
