Hukumar National Youth Service Corps (NYSC) da rundunar ‘yan sanda ta Nigeria Police Force sun sake jaddada haɗin kansu domin inganta tsaro ga ‘yan bautar ƙasa a fadin Najeriya.
Wannan tabbacin ya fito ne yayin ziyarar girmamawa da Darakta-Janar na NYSC, Brigadier General Olakunle Nafiu, ya kai hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja domin ganawa da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mr Olatunji Disu.
A yayin ziyarar, Nafiu ya taya sabon Sufeto-Janar murna tare da yabawa ƙoƙarin gyare-gyaren da ake ci gaba da yi a cikin rundunar ‘yan sanda.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin NYSC da ‘yan sanda domin tabbatar da tsaron rayuwa da dukiyar ‘yan bautar ƙasa, musamman a sansanonin horaswa da kuma al’ummomin da suke hidima.
Ya ce:
“Yan sanda sun kasance ginshiƙi wajen tabbatar da nasarar shirye-shiryen NYSC tun daga kafuwarsa.”
Nafiu ya kuma yi kira da a ƙara tsaurara tsaro a sansanonin NYSC da kuma wuraren da ‘yan hidima ke zaune a faɗin ƙasar.
Ya bayyana damuwa kan tsaro yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen 2027, inda ya buƙaci a ƙara matakan kariya ga ‘yan hidima da dukiyoyinsu.
A nasa jawabin, Sufeto-Janar na ‘yan sanda ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuwar ‘yan NYSC a duk faɗin ƙasar.
Ya kuma bayyana cewa rundunar na da bayanan wuraren da ‘yan NYSC ke zama domin saurin kai ɗauki idan bukata ta taso.
Dangane da batun takardar keɓewa ga waɗanda suka kammala karatu a Nigeria Police Academy, ya bayyana cewa za a ci gaba da tattaunawa don warware matsalar bisa ƙa’ida.
Dukkan bangarorin biyu sun yi alkawarin ƙara ƙarfafa haɗin kai domin tabbatar da tsaron ‘yan bautar ƙasa a duk fadin Najeriya.
