Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta sanar da sabbin ka’idoji da nufin rage asarar wutar lantarki a layin jigilar wuta (transmission) tare da inganta gaskiya da bin diddigi a tsarin wutar lantarki na ƙasa.
A cikin sabon umarni mai lamba NERC/2026/026, hukumar ta kafa sabon tsarin da zai inganta yadda ake auna da kuma rahoton asarar wuta a dukkan yankunan hanyar wutar lantarki a Najeriya.
Bayanan da aka samu daga Nigerian Independent System Operator (NISO) sun nuna cewa matsakaicin asarar wutar lantarki ya kasance 8.71% a shekarar 2024, kafin ya ragu zuwa 7.24% a 2025. Duk da wannan raguwar, har yanzu ya wuce matakin 7% da aka tsara a tsarin farashin wuta na MYTO.
Sabon umarnin, wanda ya fara aiki a ranar 13 ga Afrilu, 2026, ya doru ne a kan dokar Electricity Act 2023, wadda ta ba NERC ikon kula da inganci da gaskiya a fannin wutar lantarki.
Abin da sabon tsarin ya kunsa:
NISO zai girka smart meters a dukkan wuraren haɗuwar layin wuta kafin Disamba 2026
Za a rika auna yawan wutar da ke shiga da fita daga tashoshin wuta daidai
NISO zai rika gabatar da rahoton kwata-kwata ga hukumar NERC
Kamfanin Transmission Company of Nigeria (TCN) ya mika shirin rage asara kafin Yuli 2026
Ana sa ran rage asarar wuta zuwa ƙasa da 6.5% kafin Disamba 2026
NERC ta ce wannan mataki zai taimaka wajen:
Inganta yadda ake sarrafa layin wutar lantarki
Ƙara gaskiya da bin ka’ida a tsarin wuta
Taimakawa wajen saita farashi mai adalci ga masu amfani da wuta
Hukumar ta kara da cewa ingantaccen rahoton asarar wuta yana da muhimmanci wajen tsara makamashi da kuma inganta aikin tsarin wutar lantarki gaba ɗaya a ƙasar.
