Shugaban Karamar Hukumar Kosofe a jihar Lagos, Moyo Ogunlewe, ya bayyana matuƙar damuwarsa kan wani abin mamaki da ya gani a wata kasuwa da ke yankin Oworoshoki, inda aka mayar da bayan gida (toilet) wurin sayar da abinci da kuma yin salon gashi.
Rahotanni sun nuna cewa Ogunlewe ya gano wannan lamari ne yayin wata ziyara ba tare da sanarwa ba da ya kai kasuwar da ke titin Onabanjo, domin duba yadda ake gudanar da ayyuka da kuma aikin gina hanya da ake yi a yankin.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (X), an ga shugaban karamar hukumar yana zagaya kasuwar tare da tattaunawa da ‘yan kasuwa da jami’ai, inda yake nuna damuwa kan yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci a cikin wurin da bai dace ba.
Ya ce:
“Wannan bandaki ne fa! Ta yaya za a zauna ana sayar da abinci ko yin gashi a irin wannan wuri? Wannan yana da matuƙar haɗari ga lafiyar jama’a.”
Ogunlewe ya gargadi masu irin wannan hali da su daina, tare da jaddada cewa hukumomi za su ɗauki mataki domin kare lafiyar al’umma da tsaftar muhalli.
Wannan lamari ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, inda da dama ke kira ga gwamnati da ta ƙara tsaurara doka kan tsafta a kasuwanni domin kauce wa yaduwar cututtuka.
