A ci gaba da aikin rundunar Hisbah mai taken Operation Gyara Kayanka, an gudanar da sintiri a wurare kamar haka:
1. Rukunnin Gifajan Danladi Nasidi
2. Mariri
3. Hotoro
4. Banana Surut Zoo Road
5. Zariya Road
A yayin aikin, an cafke mutane biyar—mazaje uku da mata biyu—tare da wani matashi mai shekaru 25 da ake zargi da harkar bokanci.
Mataimakin Babban Kwamandan Rundunar, Dr. Mujahiddin Aminudden Abubakar, ne ya sanar da hakan, inda ya ja hankalin mata su rika kyautata wa mazajensu idan suna son su mallake su.
