Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Dokta Gbenga Olawepo-Hashim a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Accord Party a zaɓen 2027.
Mai shari’a Mohammed Umar ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, inda kotun ta kuma umarci jam’iyyar Accord Party da ta miƙa tare da ɗora sunan Olawepo-Hashim a tsarin hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, a matsayin ɗan takararta.
Hukuncin ya kawo ƙarshen wata doguwar takaddama ta shari’a kan kujerar takarar shugaban ƙasa ta Accord Party, wadda ta samo asali daga zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 30 ga Mayu, 2026.
Olawepo-Hashim ya garzaya kotu ne bayan jam’iyyar ta ƙi gabatar da sunansa ga INEC, duk da ikirarin da ya yi na cewa shi ne kaɗai ya tsaya takarar fidda gwani kuma ya samu nasara.
A yayin shari’ar, lauyansa, Henry Akunebu, SAN, ya nemi kotu ta tabbatar da nasarar da ya samu tare da tilasta wa jam’iyyar ta gabatar da sunansa ga INEC.
Lauyan ya kuma ƙalubalanci ingancin wasu takardun da aka yi amfani da su wajen nuna cewa an soke zaɓen fidda gwamin, musamman wata wasiƙar da aka ce an aika wa INEC domin sanar da hukumar cewa an soke zaɓen.
Akunebu ya ce wasiƙar ba ta ɗauke da hatimin hukuma ko cikakken sahihin alamar jam’iyyar ba, sannan ya tambayi yadda aka karɓe ta a hukumar zaɓen.
Sai dai lauyan Accord Party, T.W. Olusesi, ya dage kan cewa an soke zaɓen fidda gwamin kuma babu wani sahihin zaɓen da ya samar da Olawepo-Hashim a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Haka kuma, lauyan INEC, D.J. Gusen, ya bayyana cewa hukumar ba ta sa ido kan zaɓen fidda gwamin saboda ta samu sanarwar cewa an soke shi.
Amma Mai shari’a Umar ya yi watsi da hujjojin da aka gabatar kan soke zaɓen, tare da ƙin amincewa da wasiƙar da aka dogara da ita wajen sanar da INEC cewa an soke zaɓen.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa Olawepo-Hashim ya fito daga zaɓen fidda gwamin da aka gudanar ranar 30 ga Mayu, 2026, kuma ta umarci a ɗora sunansa a tsarin INEC.
Kafin kai ƙarar kotu, Olawepo-Hashim ya bayyana cewa ya bi dukkan matakan da ake buƙata domin shiga takarar, ciki har da biyan kuɗin fom na takarar shugaban ƙasa naira miliyan 50. Ya kuma ce ya bayar da naira miliyan 7 domin shirin rajistar mambobin jam’iyyar ta hanyar intanet.
A cikin ƙarar tasa, ya yi zargin cewa ƙin gabatar da sunansa ga INEC ya saɓa wa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, Electoral Act 2026 da kuma ƙa’idojin INEC kan zaɓen fidda gwani da gabatar da ’yan takara.
Bayan hukuncin, Olawepo-Hashim ya yaba wa kotun, tare da kiran ’yan jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin ganin Accord Party ta samu ci gaba a zaɓukan 2027.
Ya ce ya sadaukar da nasarar ga Allah, tare da gode wa mambobin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da tawagar lauyoyinsa.
Hukuncin kotun yanzu ya samar da matsayar shari’a kan takaddamar da ta shafi takarar shugaban ƙasa ta Accord Party, tare da buɗe hanyar da za a gabatar da sunan Olawepo-Hashim a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a tsarin zaɓen 2027.
