’Yar takarar gwamnan jihar Cross River a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Ambasada Nkoyo Toyo, ta ce za a iya ɗora alhakin rashin samun isasshiyar wakilcin mata a zaɓen 2027 kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Toyo ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin Morning Brief na Channels Television, inda aka tattauna kan matsayin mata da kuma ƙalubalen da suke fuskanta wajen shiga harkokin siyasa a Najeriya.
Ta zargi Majalisar Dokoki ta Ƙasa da bangaren zartarwa da rashin nuna isasshen ƙwarin gwiwa wajen kawar da matsalolin da ke hana mata samun damar shiga siyasa da kuma riƙe manyan mukamai.
A cewarta, mata a faɗin Najeriya sun shafe kusan shekaru biyu suna haɗa kai ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, tare da haɗin gwiwar sarakuna, malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki, domin neman kafa kujerun musamman ga mata a majalisun dokoki.
Ta ce manufar neman waɗannan kujeru ba neman gata ba ce, illa dai ƙoƙarin magance abin da ta bayyana a matsayin dogon tarihin rashin samun isasshiyar wakilcin mata a wuraren yanke shawara.
Toyo ta tambayi dalilin da ya sa har yanzu ba a kammala kafa dokar da za ta samar da irin wannan tsari ba, duk da cewa an shafe lokaci ana neman a samar da ita.
Ta ce idan da gaske gwamnati ta himmatu wajen ganin mata sun samu wakilci mai yawa a siyasa, ya kamata a samar da cikakken tsarin doka da zai ba su damar shiga harkokin siyasa cikin sauƙi.
Har ila yau, ’yar takarar ta soki wasu sassan tsarin zaɓe da tsarin da jam’iyyun siyasa ke bi wajen fitar da ’yan takara, tana mai cewa jadawalin da kuma tsarin tantance ’yan takara na iya ƙara wa mata wahala wajen samun damar shiga takara.
Toyo ta ce, a ganinta, akwai yiwuwar mata da dama ba za su samu nasarar tsallake matakan takara a zaɓen 2027 ba.
Ta ce idan hakan ta faru, Shugaba Tinubu zai kasance cikin mutanen da ya kamata a tambayi dalilin da ya sa aka kasa samun sauyi mai ma’ana wajen wakilcin mata.
“Idan akwai mutum ɗaya da za mu ɗora wannan kuskure a kansa, shi ne shugaban ƙasa da kansa,” in ji Toyo.
Toyo ta kuma yi kira ga Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da ta yi amfani da matsayinta wajen tallafa wa mata daga dukkanin jam’iyyun siyasa, maimakon mayar da hankali kan mata daga wata jam’iyya guda.
Ta ce Uwargidan Shugaban Ƙasa, a matsayinta na uwa ga al’umma, ya kamata ta tallafa wa mata masu neman mukaman siyasa da kuma waɗanda tuni suke riƙe da mukaman gwamnati.
Toyo ta jaddada cewa mata na bukatar samun damar shiga majalisun dokoki da bangaren zartarwa, tare da samun damar taka rawa wajen yanke shawarar da ke shafar al’umma.
Ta kuma ƙalubalanci ra’ayin cewa al’adu ne kaɗai ke hana mata shiga siyasar Najeriya, inda ta ce babban abin da ke buƙatar kulawa shi ne rashin isasshen ƙwarin gwiwar siyasa wajen aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙara wakilcin mata.
Batun ƙara wakilcin mata a siyasar Najeriya ya dade yana samun kulawa daga ƙungiyoyin mata da sauran masu ruwa da tsaki. A shekarar 2025, INEC ta bayyana cewa sauye-sauyen kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe, tare da tanadin doka na musamman, na daga cikin hanyoyin da za su iya taimakawa wajen ƙara wakilcin mata a majalisun dokoki.
