Gwamnatin Jihar Edo ta sanar da mayar da gwajin cutar zazzabin cizon sauro da maganinta kyauta a dukkan asibitocin gwamnati da ke fadin jihar, a wani mataki na inganta samun damar kula da lafiya ga al’ummar jihar.
Mai ba Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, shawara kan harkokin lafiya, Dr Andrew Iyamu, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a birnin Benin yayin wani taron bayani da gwamnatin jihar ke gudanarwa duk wata.
Iyamu ya ce Gwamna Okpebholo ya amince da wannan tsari ne domin tabbatar da cewa mazauna jihar za su iya samun gwaji da maganin zazzabin cizon sauro ba tare da fuskantar matsalar rashin kudi ba.
Ya bayyana cewa shirin zai gudana ne na tsawon shekaru biyu, bayan nan za a sake duba yadda tsarin ya kasance.
Baya ga wannan, gwamnatin jihar ta ce ta gyara cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko 65 a kananan hukumomi 18 na jihar, tare da gyara cibiyoyin lafiya na matakin sakandare 35.
Haka kuma, gwamnatin ta ce ta dauki kusan ma’aikatan lafiya 1,000 aiki domin kara karfin ma’aikatan da ke kula da lafiyar al’umma.
Daya daga cikin manyan ayyukan gyaran da aka gudanar, a cewar Iyamu, shi ne na Asibitin Eneghede General Hospital, wanda ya shafe kusan shekaru 19 yana cikin yanayi na rashin aiki. Ya ce ana kuma ci gaba da gyaran gidajen likitocin asibitin.
A nasa bangaren, Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Magunguna da Kayayyakin Lafiya ta Edo, Princess Kenny Okojie, ta ce gwamnatin jihar ta gyara rumbunan adana magunguna da aka gina tun zamanin tsohon Gwamnan Jihar, Janar Samuel Ogbemudia, wadanda suka lalace.
Okojie ta kuma bayyana cewa gwamnatin Edo na aiki tare da wasu masu zuba jari daga China domin fara samar da magunguna a cikin jihar, wadanda za a yi amfani da su a Edo tare da samar da damar kai su jihohin makwabta.
Ta ce daya daga cikin manufofin shirin shi ne rage matsalar jabun magunguna da masu shiga tsakani, tare da samar da ingantaccen tsarin rarraba magunguna ga asibitoci da bangaren masu zaman kansu.
Gwamnatin ta ce wadannan matakai na daga cikin kokarinta na inganta harkokin lafiya da kuma tabbatar da cewa al’ummar Edo na samun ingantaccen tsarin kula da lafiya.
