Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta tura wata tawagar ƙwararru zuwa Fatakwal, Jihar Rivers, domin ƙarfafa ayyukan ceto da agaji ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa.
Darakta-Janar na NEMA, Zubaida Umar, ce ta kafa tawagar da Daraktan Bincike da Ceto, Air Commodore Bature Usman, ke jagoranta domin tantance halin da ake ciki da kuma tallafa wa mutanen da ambaliyar ta shafa.
Bayan isar tawagar Fatakwal, ta duba wasu wuraren da ambaliyar ta shafa tare da kai kayayyakin agaji da hukumar ta amince da su domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa.
A lokacin ziyarar da tawagar ta kai gidan gwamnatin jihar, Usman ya miƙa kayayyakin agajin ga gwamnatin Rivers, tare da isar da saƙon ta’aziyya da damuwar hukumar kan illar ambaliyar.
Mataimakiyar Gwamnan Rivers, Ngozi Odu, ta gode wa NEMA kan abin da ta bayyana a matsayin saƙon agaji mai muhimmanci, tare da tabbatar da cewa za a raba kayayyakin ga mutanen da abin ya shafa.
NEMA ta ce matakin wani ɓangare ne na haɗin gwiwarta da gwamnatocin jihohi da sauran hukumomi wajen inganta ayyukan agaji da ba da tallafi cikin gaggawa ga al’ummomin da bala’o’i suka shafa.
