Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta samu laifin zarge-zarge 114 cikin 115 da Hukumar Premier League ta gabatar mata kan zargin karya dokokin kuɗaɗen gasar.
Jaridar The Athletic ta ruwaito cewa wani kwamiti mai zaman kansa ne ya yanke hukuncin bayan gudanar da dogon bincike kan harkokin kuɗin ƙungiyar tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018.
Rahoton ya ce an samu Manchester City da laifin zarge-zarge 114, yayin da aka yi watsi da zargi guda ɗaya.
Premier League ta shigar da ƙarar ƙungiyar a watan Fabrairun 2023, bayan kammala binciken da ya ɗauki kimanin shekaru huɗu kan zargin karya dokokin kuɗaɗen gasar.
Zarge-zargen sun shafi yanayi na tsawon kaka tara, ciki har da zargin rashin bayar da cikakkun bayanan kuɗi da kuma wasu harkokin kuɗi na ƙungiyar.
Sai dai Manchester City ta ci gaba da musanta aikata laifin, inda ta dage cewa ba ta karya dokokin Premier League ba.
A martanin da wani kakakin ƙungiyar ya bai wa The Athletic, ya ce tsarin shari’ar Premier League har yanzu bai kammala ba, kuma akwai wasu muhimman matakai da suka rage.
Kakakin ya bayyana cewa matsayin Manchester City kan zarge-zargen bai sauya ba tun bayan sanarwar da ƙungiyar ta fitar a watan Fabrairun 2023.
Ya kuma ce ƙungiyar ta mutunta tsarin binciken da shari’ar tsawon shekaru takwas, bisa tsammanin cewa hukumomin Premier League za su gudanar da aikin cikin adalci da kuma ba tare da son rai ba.
A cewar The Athletic, ana sa ran Manchester City za ta daukaka ƙarar hukuncin kwamitin.
Shari’ar dai na daga cikin manyan matakan ladabtarwa da aka taɓa gudanarwa a tarihin Premier League, kuma ta shafe shekaru ana gudanar da bincike da sauraren batun.
Zarge-zargen sun shafi wani lokaci da Manchester City ta kafa kanta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Ingila, inda ta lashe gasar Premier League da wasu manyan kofuna.
Sai dai hukuncin da aka yanke ba ya nufin an riga an tabbatar da irin hukuncin da ƙungiyar za ta fuskanta, domin za a yanke hukuncin ladabtarwa ne a wani mataki na gaba.
Ana kuma sa ran tsarin ɗaukaka ƙarar zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance ko hukuncin kwamitin zai tsaya ko kuma za a sake duba shi.
