Patrick Clancy, wani Ba’amurke wanda tsohuwar matarsa, Lindsay Clancy, ta kashe ’ya’yansu uku, ya bayyana dalilin da ya sa ya yafe mata duk da cewa ba ta taɓa neman gafararsa ba.
Patrick ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da shirin 60 Minutes na CBS News, wadda ita ce hirarsa ta farko a talabijin tun bayan da shari’ar kisan ’ya’yansu ta ƙare ba tare da juri ta cimma matsaya ba.
A yayin hirar, Patrick ya ce ya yafe wa Lindsay ne saboda ya yi imanin cewa matsalar lafiyar kwakwalwa da take fama da ita ce ta haddasa mutuwar ’ya’yan.
Lokacin da aka tambaye shi ko Lindsay ta taɓa neman gafararsa, ya amsa da cewa: “A’a. Amma na yafe mata.”
Patrick ya kuma yi watsi da wasu kalaman da kafafen sada zumunta da wasu rahotanni suka yi amfani da su wajen bayyana Lindsay a matsayin “mace mai kisa” ko “dodo”, yana mai cewa bai yarda waɗannan kalaman su ne cikakken bayanin abin da ya faru ba.
A cewarsa, ya yi imanin cewa matsalar lafiyar kwakwalwa ce ta taka muhimmiyar rawa wajen abin da ya faru.
Ya ce yafe mata ya kasance muhimmi a gare shi domin ya samu damar ci gaba da rayuwa bayan wannan mummunan lamari.
’Ya’yan ma’auratan guda uku, Cora, Dawson da Callan, sun mutu ne bayan Lindsay ta kai musu hari a gidansu da ke Massachusetts a ranar 24 ga Janairu, 2023.
Patrick ya bayyana cewa lokacin da ya dawo gida a ranar, ya tarar da Lindsay a bayan gidan bayan ta tsallake ta taga daga bene na sama, kafin daga bisani ya gano ’ya’yansu a cikin ɗakin ƙasa.
Cora da Dawson sun mutu a wurin, yayin da Callan, wanda yake da watanni takwas a lokacin, aka garzaya da shi zuwa asibitin Boston Children’s Hospital.
Patrick ya ce Callan ya rayu tsawon kwanaki huɗu, inda ya samu damar riƙe shi har zuwa lokacin da ya rasu a hannunsa.
Ya kuma bayyana cewa a cikin waɗannan kwanaki huɗu, ya rubuta saƙonnin tunawa da kowanne daga cikin ’ya’yansa yayin da yake riƙe da hannun Callan.
A cewar rahotanni, Lindsay ta shaida wa Patrick cewa abin da ya faru ya kasance kamar mafarki a gare ta, tana mai cewa tana tuna abin da ya faru kamar yadda mutum ke tuna mafarki bayan ya farka.
Shari’ar Lindsay ta ƙare da mistrial a ranar 4 ga Satumba, bayan alkalai 12 sun kasa cimma matsaya ɗaya kan ko za a ɗauke ta a matsayin wadda ke da alhakin laifin kisan.
Lauyoyin kariyarta sun yi ƙoƙarin nuna cewa tana fama da matsalar postpartum psychosis a lokacin da lamarin ya faru, yayin da masu gabatar da ƙara suka yi jayayya da hakan.
A halin yanzu, ana sa ran kotu za ta yanke shawara kan yiwuwar sake gudanar da shari’ar.
Patrick ya kuma yi magana kan jita-jitar da aka yaɗa a kafafen sada zumunta game da alhakin da yake da shi a mutuwar ’ya’yan, inda ya ce irin wannan hasashe yana cutar da abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai, wato lafiyar mata bayan haihuwa da kuma abin da ya faru da ’ya’yansa.
