Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta rarraba kayayyakin zaɓe masu muhimmanci zuwa ƙananan hukumomi uku da za a gudanar da ƙara zaɓen mazabar Gombe/Kwami/Funakaye a ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.
An gudanar da rabon kayayyakin ne a ranar Juma’a a harabar Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Gombe, a gaban wakilan jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, mambobin kwamitin tuntuba kan tsaron zaɓe da sauran masu ruwa da tsaki.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Gombe, Umar Muktar Gajiram, ya bayyana cewa an riga an kai kayayyakin zuwa ƙananan hukumomin da abin ya shafa, daga inda za a tura su zuwa rumfunan zaɓe daban-daban.
Ya ce an gudanar da aikin ne a bayyane tare da halartar dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gaskiya da kuma ƙara amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Gajiram ya kuma bayyana cewa sa hannun jami’an INEC da tabbatar da kayayyakin wani muhimmin mataki ne na tantance sahihancinsu, domin tabbatar da cewa kayayyakin da za a yi amfani da su su ne waɗanda hukumar ta amince da su.
A cewarsa, jimillar masu kada kuri’a 495,851 ne suka yi rajista kuma ake sa ran za su shiga zaɓen da za a gudanar a mazabar.
Kwamishinan ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da suka rattaba hannu a kai a hedikwatar ’yan sanda ta jihar.
Ya ce gudanar da zaɓe cikin lumana ba nauyin INEC kaɗai ba ne, domin dukkan masu ruwa da tsaki suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya da sahihancin zaɓen.
Ya kuma bayyana fatansa na cewa jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu za su mutunta alkawuran da suka dauka, tare da tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin lumana da tsari.
Add A Comment
