Jami’ar Lagos (UNILAG) na fuskantar suka daga wasu masu amfani da kafafen sada zumunta bayan fitowar mawakin Afrobeats, Fola (Folarin Odunlami), a wajen kare aikin ƙarshe na karatunsa cikin shigar da wasu suka bayyana da cewa ba ta dace da yanayin taron ilimi ba.
Hotuna da bidiyoyi da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna Fola, wanda ake cewa ya kare aikin digirinsa a Sashen Economics Education na Faculty of Education, sanye da wando mai faɗi, riga, gyale da wasu kayan ado, sannan ya isa harabar jami’ar cikin motar Cadillac Escalade.
Lamarin ya haifar da muhawara a dandalin X, inda mutane da dama suka tambayi ko jami’ar ta sassauta dokokinta saboda shahararsa a matsayin mawaki.
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa a baya an hana wasu ɗalibai kare ayyukansu saboda rashin bin ƙa’idar shigar da jami’a ta tanada, amma Fola ya samu damar gudanar da nasa ba tare da wata matsala ba.
Sai dai zuwa yanzu, Jami’ar Lagos ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba da ke tabbatar da cewa Fola ya karya dokar shigar makaranta ko kuma cewa an ba shi wata kulawa ta musamman saboda shahararsa.
