Fitacciyar mawaƙiyar Najeriya, Temilade Openiyi, wadda aka fi sani da Tems, ta kafa sabon tarihi bayan ta zama mace ta farko daga nahiyar Afirka da ta samu takardar Diamond a Amurka.
Wannan nasara ta samu ne bayan waƙar “Wait For U”, wadda ta yi tare da fitattun mawaƙan Amurka Future da Drake, ta samu takardar shaidar Diamond daga Recording Industry Association of America (RIAA).
Ana ba wa waƙa takardar Diamond ne idan ta sayar da sama da miliyan 10 a kasuwar kiɗa ta Amurka. Rahotanni sun nuna cewa waƙar ta riga ta sayar da sama da miliyan 11, lamarin da ya tabbatar da wannan gagarumar nasara.
Da wannan ci gaba, Tems ta shiga jerin kaɗan daga cikin ‘yan Afirka da suka samu wannan matsayi, inda ta haɗu da fitaccen mawaƙi Wizkid, wanda shi ma ya samu takardar Diamond sakamakon haɗin gwiwarsa da Drake a waƙar “One Dance.”
Nasarar ta ƙara nuna irin ci gaban da kiɗan Afrobeats da mawakan Najeriya ke samu a dun, iya.