Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Najeriya (CAC) ta sanar da fara shirin cire sunayen kamfanoni 100,000 daga rajistarta saboda gaza gabatar da rahoton shekara-shekara (Annual Returns) da sauran takardun da doka ta tanada.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce matakin ya biyo bayan tanadin Sashe na 692 (3) da (4) na Dokar Kamfanoni da Harkokin Kasuwanci ta shekarar 2020 (CAMA 2020).
A cewar CAC, jerin sunayen kamfanonin da abin ya shafa an wallafa su a shafin intanet na hukumar, kuma an bai wa kamfanonin wa’adin kwanaki 90 su cika dukkan takardun da suka rage tare da sabunta bayanansu.
Hukumar ta kuma buƙaci kamfanonin da suka cika sharuddan su aika shaidar bin umarnin zuwa adireshin imel da ta tanada domin tabbatar da an sabunta bayanansu.
CAC ta yi gargaɗin cewa duk kamfanin da ya kasa cika waɗannan ka’idoji cikin wa’adin da aka bayar za a cire sunansa daga rajistar kamfanoni ba tare da wata ƙarin sanarwa ba.
Hukumar ta jaddada cewa za ta ci gaba da samar da ingantattun ayyuka ga abokan hulɗarta tare da tabbatar da bin doka a harkokin rajistar kamfanoni a Najeriya.
