Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) ta saki Sister Leticia Ugboaja, ‘yar Najeriya kuma ‘yar gidan sufaye na darikar Katolika, bayan da jami’anta suka kama ta yayin da take kan hanyarta ta zuwa coci domin halartar ibadar Mass a McAllen, jihar Texas.
Sister Leticia, mamba ce ta kungiyar Daughters of Mary Mother of Mercy, kuma tana hidima a cocin Our Lady of Sorrows Catholic Church, wanda ke kusa da iyakar Amurka da Mexico.
Rahotanni sun ce kama ta ya jawo ce-ce-ku-ce bayan cocin ya wallafa labarin a shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka, ciki har da Monica De La Cruz, suka shiga tsakani domin neman a sake ta.
Mai magana da yawun Catholic Diocese of Brownsville, Brenda Riojas, ta tabbatar da cewa Sister Leticia ma’aikaciyar jinya ce mai rijista a South Texas Health System, kuma ta taba yin aiki na tsawon shekara goma a DHR Health da ke Edinburg, Texas.
Bayan matsin lambar da ‘yan majalisar suka yi ga Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS), an saki Sister Leticia tare da komawarta gida lafiya.
Har zuwa lokacin fitar da rahoton, Hukumar ICE da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ba su bayyana dalilin kama ta ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Donald Trump ke ci gaba da tsaurara matakan yaki da bakin haure ba bisa ka’ida ba, ciki har da gudanar da samame a wuraren da a baya ake dauka a matsayin wurare masu kariya kamar majami’u.
