‘Yan wasan Najeriya Rinsola Babajide da Shukurat Oladipo sun kara wani babban nasara a tarihin wasansu bayan da kungiyar AS Roma Women ta doke Juventus Women a wasan karshe na kofin Coppa Italia Women domin kammala lashe kofuna biyu na cikin gida a kakar wasa ta 2025/26.
Roma ta samu nasarar ne da ci 1-0 a wani wasa mai cike da zafi, inda ‘yar wasan tsakiya Manuela Giugliano ta zura kwallon da ta bai wa kungiyar nasara saura mintuna goma a tashi daga wasa.
Wannan nasarar ta tabbatar da kofin na biyu da Roma ta lashe a bana bayan da ta riga ta lashe gasar Serie A Femminile a farkon watan nan.
Oladipo, wacce ta kasance ginshikin tsaron Roma a duk kakar wasan, ta buga cikakken mintuna 90 a wasan karshe. Kyakkyawan bajintarta a baya ya sa aka zabe ta a matsayin mafi kyawun mai tsaron baya a gasar ta bana.
A gefe guda kuma, Babajide ba ta samu damar taka leda a wasan karshe ba, duk da cewa tana daga cikin manyan zabin kai hari na kungiyar.
Tsohuwar ‘yar wasan Liverpool Women da Rayo Vallecano Femenino ta buga wasanni 14 a dukkan gasa a bana tare da zura kwallo daya da bayar da taimakon kwallaye uku.
Ita kuwa Oladipo ta buga wasanni 31 a dukkan gasa, abin da ya nuna muhimmancinta da jajircewarta a bangaren tsaron Roma.
Wannan nasarar lashe kofuna biyu babban ci gaba ne ga ‘yan wasan biyu yayin da Roma ke ci gaba da kafa kanta a matsayin daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa ta mata a kasar Italiya.
Ga taurarin Super Falcons guda biyun, kakar wasan ta kare cikin farin ciki, lamarin da zai kara musu kima gabanin wasannin kasa da kasa masu zuwa da Najeriya.
