Rory McIlroy ya yi nasarar lashe gasar Masters a karo na biyu a jere, inda hakan ya sa ya kai ga samun kofin Major na shida a rayuwarsa.
Dan wasan golf ɗin daga Arewacin Ireland ya nuna juriya duk da cewa ya fara wasan cikin ƙalubale, inda ya yi double bogey a rami na huɗu da kuma bogey a rami na shida. Duk da haka, ya dawo da ƙarfi ta hanyar yin birdies huɗu cikin ramuka bakwai masu zuwa.
A ƙarshe, McIlroy ya kammala zagaye na ƙarshe da ƙasa da par ɗaya (one-under-par 71), inda ya kai jimillar -12 (276), ya kuma doke Scottie Scheffler da tazarar bugun guda ɗaya kacal.
Wannan nasara ta sa McIlroy ya shiga jerin manyan ‘yan wasa a tarihin Masters, inda ya zama ɗaya daga cikin ‘yan wasa huɗu da suka taɓa lashe gasar sau biyu a jere, tare da sunaye irin su Tiger Woods, Jack Nicklaus da Nick Faldo.
Bayan nasarar, McIlroy ya bayyana jin mamaki da farin ciki, yana mai cewa juriya da ya nuna tsawon shekaru a wannan gasa ne ya taimaka masa wajen samun wannan nasara.
Ya ce: “Ba zan iya gaskata cewa na jira shekaru 17 kafin in samu green jacket na farko, amma yanzu ga shi na samu guda biyu a jere.”
