Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Kwara ta tabbatar da tura ma’aikata 2,280 domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan Easter.
A cewar hukumar Jami’an za su yi aiki ne a dukkan kananan hukumomin ta 16.
Hakan na cikin Wata sanarwa da jami’in yadda labaran hukumar a jihar ta Kwara ASC I Ayoola Michael, ya fitar.
Wannan mataki yana nufin kare guraren Ibadu da wuraren shakatawa, da muhimman ababen more rayuwa daga duk wani hatsari.”
