Shahararren ɗan damben ajin masu nauyi na duniya, Oleksandr Usyk, ya bayyana yadda dangantakarsa da tsohon zakaran duniya Anthony Joshua (AJ) ta ƙara ƙarfi, inda ya ce yanzu suna yin atisaye tare domin inganta ƙwarewarsu.
Usyk, wanda ya doke Joshua sau biyu a baya, ya ce ya gayyaci ɗan damben na Birtaniya zuwa sansanin atisayensa domin su yi horo tare.
Ya ce, “AJ mutum ne mai kirki sosai, kuma yana goyon bayana a ko da yaushe. Na gaya masa idan yana buƙatar taimako zan taimaka masa. Ya zo muka yi atisaye tare na tsawon makonni biyu.”
A cewarsa, sun gudanar da atisayen damben, kariya, dabarun kai hare-hare da kuma motsa jiki a cikin ruwa, wanda ya ce ya taimaka matuƙa wajen ƙara wa Joshua ƙarfi da ƙwarewa.
Usyk ya bayyana Joshua a matsayin mutum mai jajircewa da son ƙara ilimi, yana mai cewa horon da suke yi tare yana amfanar da su duka.
Ya ce rashin aiki tuƙuru shi ne babban cikas ga duk wani ɗan wasa da ke son samun nasara.
Duk da cewa Usyk ne ya ƙwace kambun ajin masu nauyi daga hannun Joshua shekaru da suka gabata, ya ce yanzu suna da kyakkyawar alaƙa ta mutunta juna, wacce ya kwatanta da ta fitattun jaruman fim ɗin Rocky da Apollo Creed.
Usyk ya kuma bayyana cewa yana shirin taimaka wa Joshua idan ya fafata da Tyson Fury, yana mai hasashen cewa Joshua zai yi nasara ta hanyar bugun knockout kafin zagaye na shida.
Haka kuma, zakaran na Ukraine ya ce yana sa ran fafata da Deontay Wilder a wasan da zai kasance na ƙarshe a rayuwarsa ta damben ƙwararru, duk da cewa ya bayyana Wilder a matsayin ɗan dambe mai haɗari.
