Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Destiny Etiko, ta bayyana nadamarta bayan ta yi asarar Naira miliyan 5 a karon farko da ta yi caca kan wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 tsakanin Spain da Argentina.
Jarumar ta wallafa saƙo a shafinta na Instagram jim kaɗan bayan kammala wasan, inda ta ce asarar kuɗin ta girgiza ta matuƙa.
Ta bayyana cewa tashin hankalin da ta shiga yayin kallon wasan ya yi matuƙar yawa, har ta yanke shawarar cewa ba za ta sake yin caca ko kallon ƙwallon ƙafa ba.
A cikin saƙonta ta rubuta:
“Karon farko da na yi caca, kuma na yi asarar kuɗi. Ba zan ƙara gwadawa ba. Naira miliyan 5 ta tafi. Na ma daina kallon ƙwallon ƙafa, tashin hankali ya kusa kashe ni.”
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi martani kan haɗarin yin caca da manyan kuɗaɗe.
