Jami’ar University of Benin (UNIBEN) ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarta da National Institute for Sports (NIS), yayin da Mataimakin Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor), Farfesa Edoba Bright Omoregie (SAN), ya yabawa Darakta Janar na NIS, Comrade Philip Shaibu, bisa sauye-sauyen da ya kawo a Cibiyar Bunƙasa ‘Yan Wasa ta NIS da ke Abuja.
Yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai cibiyar, Farfesa Omoregie ya bayyana cewa haɗin gwiwar tsakanin UNIBEN da NIS zai taimaka wajen bunƙasa ilimin wasanni, bincike da kuma horar da ƙwararrun ‘yan wasa a Najeriya.
Ya ce jami’ar na alfahari da kasancewa abokiyar hulɗa da NIS, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa ya dace da manufofin gwamnati na bunƙasa harkokin wasanni da ilimi.
A nasa ɓangaren, Darakta Janar na NIS, Philip Shaibu, ya gode wa shugabannin UNIBEN bisa goyon bayan da suka bayar, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa zai amfani ƙasar na dogon lokaci.
Shaibu ya bayyana cewa NIS ta fara gudanar da cikakkun shirye-shiryen karatu tare da haɗin gwiwar UNIBEN, inda ake ba da National Diploma (ND), shirye-shiryen takaddun shaida (Certificate Programmes), da kuma kwasa-kwasan horas da masu koyar da wasanni.
Ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwa na daga cikin shirin ci gaban NIS na shekaru goma, wanda ke da nufin inganta ilimin wasanni, bincike, da haɓaka ƙwarewar ‘yan wasa a Najeriya.