Kaftin din tawagar Argentina, Lionel Messi, ya sake kafa sabon tarihi bayan zama dan wasa na farko mai shekaru 30 ko sama da haka da ya fi zura kwallaye a bugu guda na Gasar Kofin Duniya ta FIFA.
Messi ya kafa wannan tarihi ne bayan yawan kwallayensa ya kai takwas a gasar Kofin Duniya ta 2026, inda ya karya tarihin kwallaye bakwai da shi kansa ya kafa lokacin da Argentina ta lashe gasar a Qatar a shekarar 2022.
Wannan sabon bajinta ya kara tabbatar da irin kwarewa da hazakar Messi, wanda ke ci gaba da kafa sabbin tarihi duk da kasancewarsa cikin manyan shekaru a harkar kwallon kafa.
Messi ya taka muhimmiyar rawa wajen kai Argentina zuwa matakin kwata fainal na gasar, inda kwallayensa takwas suka zama mafi yawa da wani dan wasa mai shekaru 30 ko sama da haka ya taba ci a bugu daya na Gasar Kofin Duniya.
