Shahararren mawakin wakokin street-pop, Habeeb Okikiola, wanda aka fi sani da Portable, ya bayyana cewa yana da burin komawa makaranta domin kammala karatunsa, duk da irin nasarorin da ya samu a harkar waka.
Portable ya bayyana hakan ne a wani bangare na shirin Honest Brunch Podcast, inda ya yi magana kan rayuwarsa ta makaranta, matsalar rashin kudin makaranta da kuma yadda ya shahara a fagen waka.
Mawakin ya ce talauci ne ya tilasta masa barin makaranta, yana mai cewa a lokacin yana sayar da ruwan leda domin samun abin biyan kudin makaranta, amma daga bisani ya kasa ci gaba saboda tsadar kudin makaranta.
Ya ce har yanzu bai daina burin kammala karatunsa ba.
Portable ya bayyana cewa ya samu gurbin karatu a Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara (Kwara State Polytechnic) ta hanyar tsarin bai wa ‘yan asalin jihar fifiko, inda ya karanci Business Administration kafin ya dakatar da karatun.
A cewarsa, barin makarantar na daya daga cikin manyan abubuwan da ke damunsa har zuwa yau.
Mawakin ya kuma ce bai samu wanda zai dauki nauyin karatunsa ba, lamarin da ya sa dole ya hakura da makaranta.
Ya kara da cewa duk da bai kammala karatun jami’a ba, rayuwarsa ta canza sosai, kuma yanzu shi ne ke daukar nauyin mahaifinsa da kuma taimaka wa iyalansa.
Portable ya ce duk da cewa a baya ana kallonsa a matsayin wanda bai cika hazaka a karatu ba a cikin iyalinsu, yanzu shi ne ke ciyar da mahaifinsa, yayin da ‘yan uwansa mata su ma ke kokarin dogaro da kansu.
Ya bukaci matasa kada su yi watsi da ilimi, amma ya jaddada cewa samun takardar shaidar karatu kadai ba shi ne ke tabbatar da nasara ba.
A cewarsa, mutum na iya samun nasara ta wata hanya, sannan daga baya ya koma makaranta ya kammala karatunsa.
Sai dai, rahoton ya bayyana cewa ba a samu damar tabbatar da ikirarin Portable na cewa ya taba samun gurbin karatu a Kwara State Polytechnic ba.
