Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom ta sanar da cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a laifukan satar adaidaita sahu da kuma mallakar miyagun kwayoyi a wasu hare-haren da jami’anta suka kai bisa bayanan sirri.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Timfon John, ta bayyana cewa an kama Dominic Edet da Asuquo Etim bayan bincike kan satar wani adaidaita sahu kirar TVS mai lambar rajista AFG 094 WZ da aka sace daga gidan mai shi a yankin Afaha Itam da ke karamar hukumar Itu.
Ta ce bayan samun rahoton satar, jami’an ‘yan sanda sun fara bincike tare da sanya ido a wuraren da ake hada-hadar adaidaita sahu. Hakan ya kai ga cafke Dominic Edet tare da kwato adaidaita sahun da aka sace.
Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga cafke Asuquo Etim, wanda ake zargin ya sayi adaidaita sahun daga wani mutum da har yanzu yake gudun hijira. Rahotanni sun nuna cewa an sayar da adaidaita sahun kan kudi Naira miliyan 1.8.
A wani samame daban kuma, jami’an rundunar sun kama wani matashi mai suna Idorenyin Akpan mai shekaru 21 a wani yankin da aka dade ana zargin masu aikata laifuka na fakewa a jihar.
Binciken da aka yi masa ya kai ga gano wani kunshin sinadarin crystal methamphetamine wanda aka fi sani da “Ice”, bindigar wasa kirar revolver, guduma, filaya, tukunya mai dauke da wasu kayayyakin tsafi, kwalabe da wasu abubuwan da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Akwa Ibom, CP Baba Mohammed Azare, ya yabawa jami’an da suka gudanar da wadannan ayyuka tare da jaddada kudirin rundunar na ci gaba da yaki da masu aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani domin taimakawa wajen gano da cafke masu aikata laifuka a sassan jihar.
