Fitacciyar DJ kuma ‘yar kasuwa a Najeriya, Florence Ifeoluwa Otedola wacce aka fi sani da DJ Cuppy, ta bayyana cewa ba za ta taba auren dan Najeriya ba, tana mai cewa abin da ta fuskanta a wata dangantaka da ta yi a baya ne ya sa ta dauki wannan matsaya.
DJ Cuppy ta ce saurayin dan Najeriya na karshe da ta yi hulda da shi ya fi nuna sha’awar haduwa da mahaifinta, attajiri Femi Otedola, fiye da nuna kulawa gare ta a matsayin masoyiya.
A cewarta, hakan ya sa ta fara tantance hakikanin manufar wasu mazan da ke neman kusantarta, musamman saboda matsayinta da kuma arzikin iyalinta.
“Ba zan iya auren dan Najeriya ba. Na yi hulda da wani a baya amma abin da ya fi damunsa shi ne lokacin da zai hadu da mahaifina, wanda hakan ya sa na fara tunanin ko ni suke so ko kuma wani abu daban,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa mahaifinta ba ya takura mata wajen zabar wanda za ta aura, abin da kawai yake so shi ne ya ga ta yi aure kuma tana cikin farin ciki.
DJ Cuppy ta kuma yaba da dangantakar da ke tsakanin ‘yar uwarta Temi Otedola da mawakin Afrobeats, Mr Eazi, tana mai cewa tana farin ciki da yadda soyayyarsu ke tafiya.
Kalaman nata sun janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan soyayya, aure da kuma kalubalen da fitattun mata ke fuskanta wajen samun sahihiyar dangantaka.
