Tawagar Comoros ta samu tikitin fafatawa da zakarun Afrika, Super Falcons na Najeriya, a matakin share fagen shiga gasar Olympics ta 2028, bayan ta lallasa Sudan da jimillar ƙwallaye 30–0 a zagayen farko.
Comoros ta fara da babban nasara mai ban mamaki na 17–0 a wasan farko da aka buga a ranar 3 ga watan Yuni, sannan ta sake doke Sudan da 13–0 a wasan dawowa da aka buga kwanaki biyar bayan haka.
A wasan farko, Comoros ta fara cin ƙwallo da wuri, inda ta zura kwallo mintuna takwas bayan fara wasa, tare da ci gaba da matsa lamba har ta mamaye wasan gaba ɗaya. ‘Yan wasa tara daban-daban ne suka zura ƙwallaye a wasan.
A wasan na biyu kuwa, Comoros ta zura ƙwallaye uku a rabin farko, sannan ta ƙara wasu goma a rabin na biyu domin kammala nasara 13–0.
Da wannan sakamako, Comoros ta wuce zuwa zagaye na gaba da jimillar 30–0, inda za ta kara da Super Falcons, wacce ake ɗauka a matsayin mafi ƙarfi a ƙwallon ƙafar mata a Afrika.
Super Falcons, karkashin Justine Madugu, sun ci Senegal 3–0 a wasan sada zumunta, bayan sun kuma yi nasara 2–1 a wasan farko.
Za a buga wasannin zagaye na gaba tsakanin 5 zuwa 13 ga Oktoba, 2026, inda ƙasashen Afirka biyu za su fafata domin neman tikitin shiga gasar Olympics ta 2028 a Los Angeles, Amurka.
