Tsohon ɗan wasan Manchester United FC, Teddy Sheringham, ya fito fili yana kare tsohon kocin Tottenham Hotspur FC, Ange Postecoglou, yana mai cewa korar sa bayan kakar wasa mai cike da matsala babban kuskure ne da kulob ɗin ya yi.
Postecoglou ya bar Tottenham ne duk da cewa ya jagoranci ƙungiyar ta lashe kofin UEFA Europa League, wanda ya kawo ƙarshen dogon lokaci da kulob ɗin ya shafe ba tare da lashe babban kofi ba.
Sai dai rashin nasara a gasar Premier League, inda Tottenham ta kare a matakin 17 a kakar 2024–25, ya sa shugabannin kulob ɗin suka yanke shawarar rabuwa da shi, suna cewa sakamakon lig ɗin ba abin karɓa ba ne.
Sheringham, a cikin tattaunawarsa da Tribal Football, ya ce wannan mataki bai dace ba, yana mai zargin cewa raunin ‘yan wasan baya ne ya jawo faduwar ƙungiyar a lig.
“Ange Postecoglou yana iya zama yana tambayar kansa yanzu, ‘ta yaya na rasa aikin Tottenham?’” in ji shi.
Ya ƙara da cewa: “Sun dade ba su lashe kofi mai muhimmanci ba. Yanzu da aka samu koci wanda ya kawo kofi, sai aka kore shi. Wannan ba ya da ma’ana a ganina.”
Duk da haka, Sheringham ya amince cewa matsayi na lig ɗin ba abin alfahari ba ne, amma ya ce dabarar Postecoglou ta mayar da hankali kan lashe kofi ta yi nasara.
Ya kuma ce zai kasance abin sha’awa a ga yadda Tottenham za ta kasance da shi idan har an bar shi a kujerar horarwa.
“Kada mu koma da shi yanzu, amma ba za mu taɓa sanin abin da zai faru ba idan ya ci gaba da aiki,” in ji shi.
Korarsa ta ci gaba da haifar da muhawara a tsakanin masoya kwallon kafa dangane da ko ya kamata kulob ɗin ya ba shi ƙarin lokaci ko a’a.
