Tsohon shugaban ƙasar Amurka, Barack Obama, ya yaba da jarumta da ƙwarewar jami’an United States Secret Service bayan wani harin bindiga da ya faru a wajen taron White House Correspondents’ Dinner a Washington D.C. a daren Asabar.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Obama ya ce lamarin ya zama tunatarwa mai girma kan muhimmancin ƙin amincewa da tashin hankali a cikin tsarin dimokuraɗiyya.
Ya ce:
“Duk da cewa har yanzu ba mu san dalilin harin ba, wajibi ne mu ƙi amincewa da duk wani nau’i na tashin hankali a cikin dimokuraɗiyyarmu.”
Obama ya kuma nuna godiya ga jami’an tsaro, yana mai cewa jarumtar da suke nuna wa kowace rana ba a iya misaltawa.
Ya ƙara da cewa:
“Wannan abin ya tuna mana da irin sadaukarwa da jarumtar da jami’an Secret Service ke yi a kullum. Ina godiya gare su, kuma ina farin ciki cewa jami’in da aka harba yana cikin kwanciyar hankali.”
Abin da ya faru a wurin taron
Rahotanni sun bayyana cewa an ji karar harbe-harbe a wajen taron da aka gudanar a otel ɗin Washington Hilton, inda shugaba Donald Trump da uwargidansa Melania Trump da mataimakin shugaban ƙasa JD Vance suka halarta, tare da ‘yan jarida da jami’an gwamnati da shahararru.
Wani wanda ya shaida lamarin ya ce wani wanda ake zargi da bindiga ya yi yunkurin kutsawa wurin tsaro, abin da ya jawo rudani da gaggawar matakin jami’an tsaro.
Jami’ai sun ce an harbi wani jami’in tsaro a lokacin artabu, amma harsashin ya bugi rigar kariya (bulletproof vest) ya kuma kare rayuwarsa. Rahotanni sun ce jami’in yana cikin kwanciyar hankali a yanzu.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano dalilin harin da kuma wanda ke da alhakin abin da ya faru.
Add A Comment
