Yayin da kakar Premier League 2025/26 ke dab da kammaluwa, ƙungiyar Arsenal na kan gaba da maki 73 daga wasa 34, yayin da Manchester City ke biye da maki 70 daga wasa 33. Manchester United kuma na matsayi na uku da maki 58.
Amma idan aka duba aikin kowanne koci bisa maki a kowane wasa (points per game – PPG), sakamakon yana nuna yadda kowanne manaja ya yi daidaito da tasiri a kakar.
Matsayin manajoji bisa PPG (kamar yadda Planet Football ya ruwaito):
Michael Carrick (Manchester United – wucin gadi) – 2.17 PPG
Ya kawo sauyi mai girma tun bayan karɓar ragamar United, inda ya taimaka wajen tabbatar da tikitin Champions League.
Mikel Arteta (Arsenal) – 2.14 PPG
Ya jagoranci Arsenal zuwa saman tebur, tare da tsayayyen salon wasa da daidaito.
Pep Guardiola (Manchester City) – 2.12 PPG
City na matsayi na biyu kuma suna matsawa Arsenal a kusa sosai.
Arne Slot (Liverpool) – 1.70 PPG
Unai Emery (Aston Villa) – 1.70 PPG
Enzo Maresca (Chelsea – har zuwa sallama) – 1.58 PPG
Rúben Amorim (Manchester United – har zuwa sallama) – 1.55 PPG
Fabian Hürzeler (Brighton) – 1.47 PPG
Keith Andrews (Brentford – caretaker) – 1.45 PPG
Andoni Iraola (Bournemouth) – 1.44 PPG
Marco Silva (Fulham) – 1.41 PPG
David Moyes (Everton) – 1.38 PPG
