Midstream and Downstream Gas Infrastructure Fund (MDGIF) na tattaunawa da abokan hulɗa daga Netherlands domin samun haɗin gwiwar kuɗi wajen aiwatar da wani babban aikin samar da gas zuwa LPG da wutar lantarki mai karfin megawatt 25 a Najeriya.
Shugaban zartarwa na MDGIF, Oluwole Adama, ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Talata tare da wakilan Africa GTC Power da kuma Invest International, wacce ke ƙarƙashin gwamnatin Netherlands.
A cewar sanarwar da NMDPRA ta wallafa a shafinta na X, tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yiwuwar haɗin gwiwa wajen samar da kuɗin aikin a yankin Ikwerre, Agbada, Port Harcourt.
Aikin da ake shirin aiwatarwa zai mayar da iskar gas da ake kona (gas flaring) zuwa wutar lantarki har megawatt 25 tare da samar da LPG mai yawa domin amfanin gidaje da masana’antu.
Wannan shiri na daga cikin matakan Najeriya na sauya tsarin makamashi zuwa mai tsafta, tare da rage gurɓatar muhalli da kuma inganta samar da wutar lantarki mai dorewa a ƙasa.
Da yake jawabi a taron, Adama ya jaddada ƙudirin MDGIF na saka hannun jari a ayyukan da ke kawo tasiri kai tsaye ga tattalin arziki da rayuwar jama’a. Ya ce aikin ya yi daidai da manufofin Dokar Petroleum Industry Act 2021 (PIA), musamman wajen faɗaɗa ababen more rayuwar gas, inganta samar da makamashi, da bunƙasa ɓangaren midstream da downstream.
