Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Aerospace, Festus Keyamo, ya bayyana cewa an kirkiro wannan tsarin ne domin magance matsalolin rashin daidaiton bayanan fasinjoji da kuma hana shiga jirgi ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa:
“Tsarin VPASS zai tabbatar da cewa an tantance dukkan fasinjojin jiragen cikin gida yadda ya kamata, tare da rufe gibin da wasu ke anfani da shi wajen kaucewa ka’idojin tantancewa.”
Ya kara da cewa, yayin da aka riga aka tsaurara matakan tsaro a jiragen kasa da kasa, wannan sabon tsari zai tabbatar da cewa irin wadannan matakai sun shafi jiragen cikin gida ma.
Abubuwan da VPASS Zai Taimaka:
Inganta tsaro a filayen jiragen sama
Hana shiga jirgi ba bisa ka’ida ba
Daidaita bayanan fasinjoji
Kara kudaden shiga ga gwamnati
Inganta kwarewar fasinjoji
Yadda Za a Fara Aiwatarwa:
Ministan ya bayyana cewa za a fara ne da:
Gina kayan aikin tsarin (infrastructure)
Wayar da kan jama’a (sensitisation campaign)
Fadada tsarin har zuwa jiragen haya (private aviation)
Goyon Bayan Hukumomi:
An yaba wa hukumomi kamar:
Infrastructure Concession Regulatory Commission (ICRC)
Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN)
saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da wannan shiri.
