Gasa na neman ɗan wasan tsakiya na Morgan Rogers na ƙara zafi yayin da manyan kungiyoyin Manchester United, Arsenal, da Chelsea ke shirin fafatawa domin sayensa a wannan bazarar.
Ɗan wasan mai shekaru 23 ya taka rawar gani sosai a Aston Villa, inda ya taimaka wa ƙungiyar wajen neman gurbin shiga manyan huɗu a gasar Firimiya ƙarƙashin jagorancin kocinsu Unai Emery.
Rahotanni daga jaridar The Times sun nuna cewa Aston Villa ta sanya farashin Rogers sama da fam miliyan 80 (£80m), wanda ya kai kusan dala miliyan 108, yayin da ake sa ran kungiyoyi da dama za su gabatar da tayin sayensa.
Tun daga farkon kakar wasan da ta gabata, Rogers ya zura kwallaye 24 tare da bayar da taimako (assists) 23 a dukkan gasa, abin da ya tabbatar da shi a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘yan wasan tsakiya a gasar Firimiya.
Ana sa ran darajarsa za ta ci gaba da ƙaruwa yayin da yake shirin wakiltar ƙasar Ingila a gasar cin kofin duniya ƙarƙashin sabon koci Thomas Tuchel.
Ƙarin dalilin tsadar farashinsa shi ne yarjejeniyar kaso (sell-on clause) da aka sanya lokacin da ya koma Aston Villa daga Middlesbrough a watan Fabrairu na 2024 kan kuɗi fam miliyan 15.
