Mai magana da yawun ƙungiyar masu tace danyen mai a Najeriya (CORAN), Eche Idoko, ya bayyana cewa ƙungiyar ta dade tana kira da a samar da tsarin farashin danyen mai na cikin gida wanda ya dace da halin da Najeriya ke ciki.
A wata hira da aka yi da shi, Idoko ya ce bai kamata a rika amfani da farashin Brent a matsayin ma’auni wajen sayar da danyen mai ga matatun cikin gida ba.
Ya ce amfani da Brent yana jawo abubuwan da ba su da alaƙa da kasuwancin cikin gida su rika shafar farashin mai a Najeriya.
“Idan kana amfani da Brent wajen ƙididdige farashin mai, abubuwan da ke shafar Brent za su shafi farashin da ake sayar da mai a nan gida. Abin da muke so shi ne a cire waɗancan abubuwan da ba su da tasiri a kasuwancin cikin gida, domin a samu ainihin farashin mai ga matatun cikin gida,” in ji shi.
Idoko ya ƙara da cewa rage waɗannan kuɗaɗen zai taimaka wajen rage farashin fetur ga al’umma.
Har ila yau, ya bukaci gwamnati ta rage wasu kuɗaɗen haraji da ake karɓa a tashoshin mai ta hannun hukumomi kamar NUPRC da NMDPRA, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage tsadar mai.
“Ko da yake kuɗaɗen ba su da yawa, amma saboda kasuwancin mai yana da ƙaramin riba, cire su zai taimaka sosai. Ba muna cewa a cire su gaba ɗaya ba ne,” ya ƙara.
Ya jaddada cewa ya kamata farashin danyen mai ga matatun cikin gida ya dogara da yanayin cikin gida, ba wai na kasuwannin duniya ba.
A ƙarshe, Idoko ya ce ƙara yawan samar da mai zai taimaka matuƙa idan gwamnati ta aiwatar da dokar samar da danyen mai ga matatun cikin gida (Domestic Crude Supply Obligation).
