gagarumin farin ciki ya bayyana a jihar Kano bayan dalibai uku daga makarantar Rumfa College suka lashe gasar kasa ta nazarin tarihin Shehu Usman Dan Fodio da aka gudanar an Abuja.
Gasar wadda ta haɗa jihohi 17 na Arewa, ta nuna hazakar matasan Kano inda suka samu kashi 96% na maki gabaɗaya.
> “Mun yi nasara ne saboda muna jin dadin tarihinmu. Shehu Dan Fodio ya ba mu abin alfahari,” in ji ɗaya daga cikin daliban da suka yi nasara.
Gwamnatin Kano ta sha alwashin ba su kyautar karatu da tallafi na musamman domin ci gaba da hazakarsu.