A ranar Asabar, 13 ga Yuli, 2025, Allah Ya karɓi ran tsohon shugaban Najeriya, Major General Muhammadu Buhari (rtd.), yana da shekara 82 a duniya. Ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin London, bayan gajeruwar rashin lafiya.
Sanarwar ta fito daga bakin kakakin iyalinsa, Mallam Garba Shehu, wanda ya tabbatar da hakan da safiyar yau.
“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Iyalin marigayi Muhammadu Buhari sun tabbatar da rasuwarsa. Allah Ya gafarta masa Ya saka masa da alheri,” inji Garba Shehu.Marigayi Buhari ya rike mulki a matsayin:
Shugaban Soji (1983 – 1985)
Shugaban Ƙasa na Dimokuradiyya (2015 – 2023)
An san sa da:Yaƙi da cin hanci da rashawa
Ƙarfafa bangaren tsaro
Ƙoƙarin farfado da tattalin arziki
Da kuma kasancewa mai tsantsar gaskiya da haƙuri
🤲🏼 TA’AZIYYA
Asrah 24 TV na mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan marigayin, jama’ar Najeriya da dukkan masoyansa a ciki da wajen ƙasa.
