Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sunan Kano State Sports Commission zuwa Kano State 22 Athletes Sports Commission, tare da sauya Kano State Sports Institute zuwa Kano State 22 Athletes Sports Institute.
Wannan mataki yana cikin shirin tuna da ’yan wasan Kano 22 da suka rasu a haɗarin mota a kan hanyar Kano-Zaria a watan Mayu.
Gwamna Abba ya ce, “Wannan canji zai kasance abin tunawa har abada domin girmama rayukan da suka sadaukar da kansu wajen wakiltar jihar Kano.”
🟦 Asrah 24 TV – Gaskiyar zance.
