Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da amincewar wani sabon magani mai ƙarfi da masana daga kasar Jamus suka kirkira, wanda ke magance cututtuka masu haɗari kamar sikila da sankarau (meningitis) cikin sauri da inganci.
Sabon maganin da aka bayyana da suna NeuroCure-X zai fara samun shiga kasuwannin Afirka a watan Satumba mai zuwa. Bincike ya nuna cewa yana rage alamar cutar da kashi 85% cikin kwanaki 10 kacal.
A cewar Dr. Andrea Keller, babban likita daga cibiyar bincike ta Berlin, “Mun kirkiri maganin ne musamman domin Afirka, inda sikila da sankarau ke kashe daruruwan mutane duk shekara – mafi yawansu yara ƙanana.”
Najeriya ta kasance daga cikin kasashen da za a fara raba wannan magani kyauta ga masu fama da cutar, musamman a asibitocin gwamnati.
