An shiga cikin wani yanayi na tashin hankali da damuwa a yau, bayan da wani yaro ya hau kan wani karfen talla da ke kusa da gadar Lado a jihar Kano, yana ki saukowa duk da kiran jama’a da jami’an tsaro.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau, inda yaron ya haura saman karfen talla da ke kallon hanyar babban titi, lamarin da ya janyo cinkoso da tsayuwar wucin gadi ga zirga-zirgar ababen hawa.
Duk kokarin da ‘yan sanda da jami’an hukumar kashe gobara (kwana-kwana) suka yi na lallasar yaron ya sauko, ya ci tura. Yaron ya dage cewa ba zai sauko ba sai an kira masa shahararren mai nishadantarwa a TikTok, Abdul BK.
Cikin sa’o’i kadan, rahotanni suka isa ga Abdul BK wanda ke daga cikin fitattun ‘yan TikTok a Kano. Da isowarsa, yaron ya fara sakin jiki, inda daga bisani ya sauko cikin salama tare da rungumar jarumin nishadin.
